Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Yaki Da Cin Hanci Ta Kasa Da Kasa Ta Fidda Rahoto


Wani mutum yana wuce tambarin yaki da cin hanci da rashawa a Abuja, Nigeria August 28, 2015.
Wani mutum yana wuce tambarin yaki da cin hanci da rashawa a Abuja, Nigeria August 28, 2015.

kimanin mutanen nahiyar Afirka miliyan 75 suka kasance cikin cin hanci da rashawa a shekarar da ta gabata

Kungiyar yaki da cin hanci ta kasa da kasa Transparency International, ta kiyasta kimanin mutanen nahiyar Afirka miliyan 75 suka kasance cikin cin hanci da rashawa a shekarar da ta gabata, a wani rahoto da yake cewa yawancin ‘yan Afirka sunyi imanin cin hanci da rashawa na ‘kara kazancewa.

Masu bincike sun tambayi mutane sama dubu 43 dake nahiyar Afirka, kan saninsu da kuma yadda suke ganin cin hanci da rashawa. kashi 53 cikin dari na mutanen sunce sunyi Imanin cewa cin hanci da rashawa ya karu a kasashen su cikin watanni 12.

Yawacin shugabannin Afirka sunyi kamfen ne da ‘daukar alkawarin shawo kan matsalar cin hanci da rashawa, amma da alamu har yanzu matsalar na kara yawaita a nahiyar Afirka.

Da yawa mutanen da akayi wannan bincike da su, sun fito ne daga kashen Afirka 18 kuma sunce gwamnatocin su basa tabuka abin kirki wajen yaki da cin hanci da rashawa, musammam ma yafi yawa ga jami’an kotu dana ‘yan sanda.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG