Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar 'Yan Jarida Mata Ta Gudanar Da Taronta Na Kasa a Jos


Taron 'yan jarida mata na kasa a Jos
Taron 'yan jarida mata na kasa a Jos

Taron kungiyar mata 'yan jarida a Najeriya na wannan shekarar an gudanar dashi ne a Jos babban birnin jihar Filato, taron kuma ya mayar da hankali ne akan wahalar da mata ke shiga da zara mazajensu sun rasu saboda wasu al'adu da dokoki.

Kungiyar 'yan jarida mata ta gudanar da taronta na kasa inda ta jaddada aniyarta na dakile matsalolin da mata da yara ke fuskanta, musamman matan da suka rasa mazajensu.

Taron wanda ya tattaro 'yan jarida mata daga jihohin Najeriya 36 da babban birnin Abuja ya tattauna ne akan matsalolin da mata da marasa galihu ke fuskanta a kasar da zummar samo hanyoyin warwaresu..

Madam Jennifer Yarima ita ce shugabar 'yan jarida mata a jihar Filato ta ce sun gayyato mai jawabi ne wanda ya yi masu jawabi akan matsalar matan da mazajensu basu suke sha a hannun 'yanuwan mazajensu. Da zara mazajensu sun mutu sai a hanasu kadarorinsu. 'Yan mata marayu kuma walau su yi aure da wuri ko kuma a dinga nuna masu halayen banza. Manufar taron shi ne su lalubo bakin zaren kawar da matsalar tare da nunawa duniya abubuwan dake faruwa.

Tsohon shugaban hukumar gidauniyar tallafawa ilimin manyan makarantun Najeriya Farfesa Suleiman Bogoro ya ce kowa nada gummawar da zai bayar wajen tallafawa mata. Ya kira a gyara wasu al'adu da dokoki, mata 'yan jarida kuma su ci gaba da fada, kada su gaji, injishi.

A saurari rahoton Zainab Babaji da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG