Accessibility links

Kungiyar 'Yan Jihadi MUJAO'S Ta Kwace Birnin Gao A Arewacin Mali.

  • Aliyu Imam

Mabiya kungiyoyin sakai na Islam a arewacin Mali suke ganawa da wakilin ECOWAS, Blaise Compaore a Ougada

Kwana daya bayan mayakan sakai masu kishin Islama suka kwace birnin Gao dake arewacin Mali daga hanun ‘yan tawayen Abzinawa, biyo bayan gwabza fada da suka wanda da ya halaka akalla mutane ashirin.

Kwana daya bayan mayakan sakai masu kishin Islama suka kwace birnin Gao dake arewacin Mali daga hanun ‘yan tawayen Abzinawa, biyo bayan gwabza fada da suka yi wanda ya halaka akalla mutane ashirin. A yanzu haka akwai rahoto dake nuna cewa mayakan kungiyar Islama suna tururuwa zuwa binrin na Gao.

Kungiyar mai alaka da al-Qaida, kuma ake kiranta MUJAO’s, watau hadakar kungiyar masu jihadi a yammacin Afirka, ta kwace iko kan birnin na GAO baki daya, daga hanun kungiyar ‘yan tawayen abzinawa da ake kira da lakanin MNLA a jiya laraba.

Wakilin sashen faransa na Muriyar Amurka ya fada yau Alhamis cewa, ko ta ina sai bakar tutar kungiyar MUJAO kake gani a birnin na GAO. Haka kuma ya aiko mana da rahoton cewa wata kungiyar ita mai da’awar Islama ta Ansar Dine, ta kawo gudumawar mayaka fiyeda dari zuwa birnin, domin tallafawa kungiyar MUJAO.

XS
SM
MD
LG