WASHINGTON, DC —
Kungiyar 'Yanuwa Musulmi, ranar tunawa da Nana Fatima da aka gudanar a Abuja, tayi soma tabi akan fim da take yi akan tarihin Shehu Dan Fodio.
Kungiyar ta nuna shirin taba ka lashen ne a taron tunawa da ranar Nana Fatima na bana a Abuja. Kungiyar da ta nuna juyayi akan cigaba da garkuwa da 'yan makarantar Chibok tace mata sun bada gudunmawa wajen gina al'umma suna bada misali da yadda Nana diyar Shehu Dan Fodio ta ilmantu kuma ta ilmantar.
Babbar bakuwa a taron Zinatudeen Ibrahim El-zazzaki ta gabatar da lacca ne kan Nana Fatima diyar manzo daga uwargidansa Khadijatu Kubura. Wani daratsi babba da za'a dauka daga Nana shi ne yadda ta yaki zalunci domin yanzu ana zaune ne a wani irin yanayi inda azzalumai suke tafiyar da al'amarin mutane, suna zaluntar mutane kuma suna dandannesu. Yadda ta tashi ta yaki zalunci haka ma yakamata mata su tashi su yaki zalunci.
Idan da mata da maza zasu yi koyi da Nana Fatima da adalci ya tabbata. Shi ma sakataren babban masallacin Abuja Ibrahim Muttawalin Jega ya karfafa mahimmancin taron. Yace wajen gefen wa'azi yakamata Malama Zinatudeen ta zama abun koyi. Ba wai kawai mata su zauna gida ba, babu karatu babu komai. Mata suna da cikakkiyar dama su nemi ilimi a kowane fanni a kowane wuri. Ta bada kasida kuma abun da ta bayar abun koyi ne ga kowace diya mace musulma.Mata suna da tasiri a wajen tarbiyar yara.Maza basa zama gida na wani tsawon lokaci a rana guda. Mata ko uwa ita take tare da yara.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.