Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gane Motar da Aka Kai Hari da Ita a Kano


Harin bom da aka kai Kano.

Maharan da suka kai hari sabon garin Kano sun ajiye motar ne sukayi tafiyarsu babu maharin a ciki

A wani harin bom din da aka kai a sabon garin kano,a daren jiya abunda ya fito fili yanzu shine an gane wace irin kiran motace sukayi amfani da ita wajen kai wannan harin.

Wani babban jami’in soja da wakilin mu Muhammadu Salisu Rabiu ya zanta da shine ya shada masa cewa motar da aka yi amfani ita Toyota Sienna ce, yace kuma wadanda suka dauko boma-bomai sun so su shiga wajen wani shakatawa ne kusa da wurin da bom din ya tashi amma masu gadin suka hanasu .

Watakila ganin cewa bom din ya kusa tashi yasa suka barshi a bakin titi sukayi tafiyarsu, shi babban jami’in ya nuna ma wakilin hotunan wasu daga cikin wadanda suka rasa rayukansu sandiyar tashin bom din,akwai mutane uku da kuma wata yariya ‘yar shekaru goma.

Shi babban jami’in sojan da wakilinmu ya zanta dashi yace maharan sun ajiye motar ne sukayi tafiyarsu bai nuna cewa akwai maharin a ciki ba,Wannan shine wani sabon abunda ya bayyana zuwa yau.
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:40 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG