Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Fafutika Sun Gana da Majalisar Dokokin Niger Akan Kasafin Kudi


Majalisar ministocin Niger mai mambobi 43 na cikin korafin da kungiyoyin fafutika suka yi a kai domin ana bata kudin kasar akan ministocin
Majalisar ministocin Niger mai mambobi 43 na cikin korafin da kungiyoyin fafutika suka yi a kai domin ana bata kudin kasar akan ministocin

Hadakar kungiyoyin dake fafutika a Niger sun gana da ‘yan majalisar dokokin Niger bisa ga kurakuran da suka ce na tattare da kasafin kudin da gwamnati ta gabatar

Tun lokacin da gwamnatin Niger ta gabatar da kasafin kudin shekara mai zuwa ‘yan kasar suka soma cece kuce akai musamman saboda harajin da aka dorawa kudin rabon gado.

Sakataren hadakar kungiyoyin shi ya yiwa ‘yan jarida bayani akan ganawarsu da ‘yan majalisar kasa dangane da cece kucen da ya biyo bayan kasafin kudin 2018.

Nuhu Muhammadu Arzika y ace sun nunawa ‘yan majalisar kurakuren dake cikin kasafin. Y ace idan ‘yan majalisar sun ji kukan jama’a sun yi gyara zasu goyi bayansu. Idan kuma suka ki to ala tilsa zasu bisu har sai sun gyara. Y ace sub a zasu bari ba, kokawa ma zasu yi.

A bayanan da suka bayar kungiyoyin sun ce sun gano wasu matakai dake jawowa kasa hasarar miliyoyin sefa har dubu hamsin da biyar, 55,000m, kowace shekara daga harajin da gwamnati ke shirin yafewa wasu manyan kamfanoni dake zaman kansu. Wani abun da suka lura dashi kuma shi ne yawaitar dawainiyar gwamnati.

Malam Ali Idrisa shugaban kungiyar ROTAB y ace ana barna da kudin kasa akan ministoci har 43. A cewarsa sun yi yawa ga kasa matalauciya irin Niger. Kamata yayi a kashe kudi akan ilimi da kiwon lafiyar jama’a da ayyukan gona.

Da alama ‘yan majalisar kasar sun gamsu da bayanan kungiyoyin fafutika. Sun amince abubuwan da kungiyoyin suka fada gaskiya ne.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG