Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Fararen Hula Sun Rena Taimakon Gwamnati Ga Wadanda Ambaliyan Ruwa Ya Shafa


Wasu da ambaliyan ruwa ya rabasu da muhallansu
Wasu da ambaliyan ruwa ya rabasu da muhallansu

Kungiyoyin fararen hula sun rena irin taimakon da gwamntin Nijar ta baiwa mutanen da ambaliyan ruwa ya rutsa da muhallansu da gonakinsu

A cewar kungiyoyin fararen hulan Nijar taimakon da gwamnati take baiwa wadanda al'amarin ambaliyan ruwa ya shafa a kasar bai taka kara ya karya ba.

Suna mai cewa kamata yayi gwamnati ta kebe wasu kudade na musamman da zata fara yin anfani dasu idan an samu irin wannan matsalar duk shekara.

Alhaji Idi Abdu daya daga cikin masu fafutika cikin kungiyoyin fararen hula a Nijar ya yi misali da kasar Amurka da ambaliyan ruwa ya samu birnin Houston, shugaban kasar Amurka ya gayawa 'yan majalisar kasar su gaggauta su fitar da kudi daga asusun ko-ta-kwana. Yace ya kamata a ce Nijar ma tana da irin wannan asusun.

Ya cigaba da cewa yanzu basu ga wata alama gwamnati na fito da kudi muraran domin taimakawa mutanen da bala'in ya shafa ba kuma su san an taimaka masu.Kamata yayi kafin wasu su fito daga ketare da taimako gwamnatin kasar ta yi iyakacin kokarinta.

Sai dai duk da korafe kofaren kungiyoyin, gwamnatin kasar na cigaba da taimakawa wadanda ambaliyan ruwan ya shafa. Gwamnan Yamai Bello Jatau Ali yace gwamnati ta kawo taimako mai dimbin yawa ga wadanda suka rasa gidajensu.

Ga rahoton Yusuf Abdullahi da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00

Facebook Forum

Hira Da Dakta Faruk Bibi Faruk Akan Matsalar Tsadar Rayuwa A Najeriya Kashi Na Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG