Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kura Ta Lafa a Rikicin Taraba


Kwamishinan 'Yan sanda Jihar Taraba, Mr. Yakubu Yunana Babas
Kwamishinan 'Yan sanda Jihar Taraba, Mr. Yakubu Yunana Babas

Bayan rikicin kabilancin da ya barke a yankin Mambila dake jihar Taraba rundunar ‘yan sandan jihar ta ce yanzu hankula sun kwanta.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ASP David Misal, ya fadawa sashen Hausa na Muryar Amurka cewa tun daga jiya ba a sake jin wani sabon tashin hankali ba.

“Abin ya lafa, domin tun jiya har kawo yanzu, ba mu sake jin wani mummunan bayani ba, kuma jami’an tsaro suna nan kuma duka kowa (masu gudun hijra) ya koma gidansa.”

Kakakin ‘yan sanda ya ce yanzu haka mutum biyar ne suka shiga hanu wadanda ake zargin suna da hanu wajen ta da tarzomar.

Ya kara da cewa adadin mutanen da aka tabbatar da mutuwarsu mutum uku ne.

“Kawo yanzu mun tabbatar da mutum uku da suka rasa rayukansu.” In ji ASP Misal.

Sai dai dan majalisar dokokin jihar mai wakiltar yankin Nguroje, Barrister Muhammad Bashir Bape, ya ce akwai bukatar jami'an tsaro su kara sa ido a yankunan da ake rikicin domin akwai wadanda suke kai harin sari-ka-noke.

“Har yanzu a sare-saren shanu a daji, har yanzu muna nan muna kokarin mu ga cewa an tura jami’an tsaro su je su ga an hana masu sarar shanun nan.” In ji Bape.

Rikicin ya barke ne a ranar Lahadin da ta gabata a tsakanin kabilar Kakas da Fulani a Gembu, Nguroje da wasu yankunan karamar hukumar Sardauna dake jihar ta Taraba wacce arewa maso gabashin Najeriya.

Saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz domin jin cikakken bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG