Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kurdawa da Daular Islama ko ISIS Suna Gwabza Fada a Kobani


Tankunan yakin Turkiya sun ja daga akan iyaka da Syria
Tankunan yakin Turkiya sun ja daga akan iyaka da Syria

Mayakan sa kai na kurdawa da mayakan ISIS suna gwabza fada a garin Kobani dake kan iyaka da kasar Syria da Turkiya

Mayakan sakai na kurdawa da na kungiyar ISIS suna gwabza yaki kan tituna domin iko kan garin Kobani dake kan iyakar Syria da Turkiyya.

Kungiyar dake ikirarin rajin kare hakkin Bil’Adama a Syria mai cibiya a Ingila tace an kashe akalla mayakan sakan ISIS 27, da kuma 19 na kurdawa tsakanin Lahadi da jiya Litinin, ciki har da wata ‘yar gwagwarmayar kurdawa wacce ta tarwatsa kanta ta kashe wasu mayakan sakan ISIS masu yawa sakamakon haka.

A jiya Litinin daga wani tsallake a Turkiyya an hango bakar tutar kungiyar ISIS kan wani gini a Kobani.

Amma wani jami’in tsaron Kurdawa yace mayakansu zasu ci gaba da yaki da Turjiya har Mahdi ya bayyana. Yace idan har ISIS ta kama garin Kobani to garin zai zama makabarta.

Yakin da ake gwabzawa ya tilastawa dubban fararen hula tsallakawa zuwa Turkiyya.

Kakakin sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban ki-moon yace Mr. Ban ya damu ainun kan farmakin da ISIS take kaiwa Kobani. Daga nan yayi kiran gaggawa ga duk wadanda suke da hali su taimaka wajen kare fararen hula.

XS
SM
MD
LG