Accessibility links

Masu fama da cutar kuturta a jihar Niger sun koka sakamakon rashin isasshen magani

Masu fama da cutar kuturta a jihar Niger sun koka sakamakon rashin isasshen magani ,kasancewa babban asibitin jinyar cutar kuturtar dake Minna babban birnin jihar yana fama da karancin magani da rashin isassun kayan aiki da ma’aikata.

Matsalolin da majinyatan ke fuskanta kuma sun hada da rashin kyaun hanyar zuwa asibitin dake tazarar kilomita biyar daga Minna fadar jihar.

Sarkin kutaren Suleija , wanda kuma ya kasance shugaban kungiyar kutaren jihar Niger mallam Mohammadu Musa ya bayyana cewa, masu fama da cutar kuturtan basu samu magunguna yanzu a kan lokaci kamar yadda aka saba a da, ya kuma yi kira ga hukumomi su dauki matakan shawo kan matsalar.

Da yake maida martani, Dr. Ibrahim Ndasu babban likitan kutaren ya bayyana cewa, gwamnati ta dauki nauyin ciyar da majinyatan da basu da karfin aljihu yayinda ta kuma sa hanyar a kasafin kudin bana da nufin gyarawa.

Likitan ya kuma yi kira ga masu hali baiwa su taimaka domin bisa ga cewarshi, gwamnati ba zata iya daukar nauyin jinyar masu fama da cutar kuturtar ita kadai ba.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG