Yanzu maki 8 ne tsakanin Inter Milan da ke saman teburin gasar da Juventus wacce ke da maki 45 yayin da Inter ke da maki 53.
Yanzu babu wanda ya fi Ronaldo yawan kwallaye a gasar ta Serie A a wannan kakar wasa, hakan na nufin ya wuce Romelu Lukaku na Inter Milan a yawan kwallaye.
Kwallaye 18 Ronaldo ya ci a wannan kakar wasa.
An tashi a wasan ne da ci 3-0, Weston McKennie ne ya ci wa Juventus kwallonta ta uku yayin da Ronaldo ya ci biyu.
AC Milan ce ke biye da Inter a teburin gasar ta Serie A da maki 49 yayin da Roma ke matsayi na hudu da maki 44.
A halin da ake ciki kuma a ranar Talata za a kara a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai tsakanin Chelsea da Atletico Madrid.
Dubi ra’ayoyi
Ko ka yi rijista da mu? Shiga shafinka
Ba ka yi rijista da mu ba? Yi rijista
Load more comments