Accessibility links

Kwamandojin Boko Haram Sun Bar Shekau Cikin Rana


Wakilan kungiyar Boko Haram ta Najeriya

Kwamandojin Boko Haram Sun Bar Shekau Cikin Rana lamarin da ya fito fili a zantawar da wakilin Muryar Amurya ya yi da su.

Wasu kwamanadojin kungiyar Boko Haram sun fadawa wakilin Muryar Amurka a Abuja cewa basa tare da shugabansu Abubakar Shekau lamarin da ya karfafa abubuwan da Mohammed Marwana ya fada tun can farko.

''Yan majalisar kolin kungiyar da ake kira Shura sun ce yanzu Abubakar Shekau ya rasa goyon bayansu domin neman zaman lafiya suka sa a gaba. A wata sanarwa da suka fitar sun ce lokaci ya yi da yakamata a zauna a nemi sulhu da gwamnatin tarayyar Najeriya kamar wani daftari da suke ce sun baiwa gwamnati a ranar 26 na watan Yunin wannan shekarar. Kwamandojin ko shugabannin sun hada da Abdullahi Hassan tsohon shugaban tsaro na Malam Shekau da Imam Abubakar Abu da Abu Zamira Mohammed wanda shi ne jami'in hulda da jama'a da watsa labarai na kungiyar da Abu Adam Maisandari walin kungiyar da Kassim Imam Biu da Abu Abubakar ibn Yusuf ko Baba Sani da kuma Babban Kwamanda Malam Modu Damaturu waddanda dukansu na cikin kwamitin kolin kungiyar da ake kira Shura.

A zantawar da aka yi dasu daya bayan daya sun ce ko shakka babu Shekau ya yi asarar manyan askarawansa. Yanzu shi kadai yake. Sun ce sun yi kokarin su gana da shi amma kokarinsu ya cutura domin bab
u wanda ya san inda ya ke. Sun ce ko ya yarda ko kada ya yarda duk daya domin basa tare da shi. Yakin da suke yi domin Allah ne kuma babu inda aka ce a addinance kada su nemi sulhu da makiyansu. Suna son Musulmai su zauna lafiya musamman wuraren da suka shiga wahala sanadiyar abubuwan da suka rika yi.

Umar Faruk Musa nada rahoto.

XS
SM
MD
LG