Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamishanan 'Yansandan Filato Yayi Karin Haske Akan Fashewar Bamabamai a Jos


Mutane na kallon wajenda Bom ya fashe a birnin Jos, dake Jihar Filato.

Yayin da ake zaton za'a shawo kan 'yan Boko Haram masu haddasa ta'adanci sai gashi wasu bamabamai sun tarwatse a tsakiyar birnin Jos fadar gwamnatin jihar Filato.

Kawo yanzu mahukunta a jihar Filato sun tabbatar da mutuwar mutane dari da goma sha takwas wasu da dama sun jikata. Adadin wadanda suka rasa rayukansu ka iya karuwa idan an gama kwashe baraguzan motoci da gidaje da lamarin ya rutsa da su.

Kwamishanan 'yansandan jihar Chris Olape yayi karin haske akan yadda aka kai harin bamabaman jiya da misalin karfe uku na rana. Motoci biyu dauke da bamabaman suka tarwatse a daidai inda aka samu cunkoson motoci da ababen hawa kan hanyar kasuwar dake tsakiyar garin Jos, wato kasuwar taminus.

Dan kunar bakin wake na farko da ya kawo kusa da kasuwar inda ake da cunkoson motoci sai ya fito yayi kamar zai duba abun da ya hana motoci tafiya kana ya koma cikin motar kirar fiat ya tayar da bam nan take ya rigamu gidan gaskiya. 'Yan mintuna ashirin zuwa talatin da tashin bam na farko sai kuma wani dake tuka motar bas kirar siyena shi ma ya tsaya a tsakiyar hanya yayi ta kare sai bam ya tarwatse daga cikin motar. Tazarar dake tsakanin motocin biyu bai fi kafa dari ba.

Kwamishanan 'yansandan ya bukaci jama'a da su guji zuwa wurin da bam ya tashi idan kuma suna kusa da wurin su kwanta kasa har na tsawon mintuna talatin kafin su tashi. Kwamishana Olape ya roki jama'a idan suna da bayanai su bayar domin su taimaki binciken da hukumomin tsaro keyi. Kana ya roki 'yan kasuwa da su dakata zuwa kasuwar har sai 'yansanda sun gama shara da bincike.

Kwamishanar yada labarai ta jihar Filato Madam Olivia Dazem ta roki jama'a da su kwantar da hankali akan lamarin da ya faru. Tace gwamnan jihar wanda yanzu baya gida ya kira ya jajantawa jama'arsa. Mataimakin gwamnan wanda shi ne ke rike da jihar shi ma yana karbar rahotanni kuma zai yi jawabi yau da nufin fadakar da jama'a.Kwamishanar tace suna rokon jama'a su taimaka da addu'o'i domin Ubangiji Yayi taimako.

Ga rahoton Zainab Babaji.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG