Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Gano Shanun Sata Yana Tantance Masu Dabbobin


Shanun da aka gano daga barayin shanu wadanda rundunar 'yansandan Kano ta dankawa kwamitin gano shanun sata da gwamnatin jihar ya kafa
Shanun da aka gano daga barayin shanu wadanda rundunar 'yansandan Kano ta dankawa kwamitin gano shanun sata da gwamnatin jihar ya kafa

Biyo bayan yawan sace-sacen shanu da dabbobi da ake yi a wasu jihohin arewa kwamnatin Kano ta kafa kwamitin gano shanun da kuma tantance masu su ta mayar masu

Kawo yanzu kwamitin ya tantace mutane 68 daga jihar Kaduna da mutane 48 daga jihar Katsina da mutane 11 daga jihar Jigawa da mutane uku daga jihar Bauchi da mutum daya daga Sokoto da 10 daga Zamfara da hudu daga jihar Neja da biyu daga Adamawa da daya daga jihar Filato,

Duk wadanda aka lissafa kwamitin yace ya tantancesu amma saboda gujewa cakudewa sun dauki rabon hawa biyu saboda sun tantance 'yan jihar Kano mutane 103. 'Yan kwamitin na kyautata zaton shanun 'yan Kanon suna cikin wadanda aka gano yanzu da suke hannunsu.

Onarebul Murtala Sulengaro shugaban kwamitin ya bayyana adadin shanun da jami'an tsaro suka danka masu. An basu a rubuce adadin dabbobi 818 sai kuma wasu 218 da suka kara samowa daga barayi kwanaki biyu da suka gabata.

Sace shanu daga Fulani makiyaya a yankin arewa wani abu sabo ne da ya kunno kai dalili ke nan gwamnan Kano Dr Ganduje yace gwamnonin arewa na hada karfi da karfe su yaki wannan sabuwar annobar.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG