Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Lafiya Ya Bukaci A Rika Yiwa Wadanda Suka Manyanta Gwajin Cutar HIV

Wani ma'aikacin asibiti yana bayani

Wani kwamiti a Amurka yayi kira ga kowanne ba-Amurke tsakanin shekara 15 zuwa 65 yayi gwajin cutar HIV, domin kiyayesu daga hatsarin kamuwa da cutar. Bisa ga cewar kwamitin wannan kuma zai rage irin yadda mutane suka daukar cutar.

Shugabannin kwamitin kwamitin gwamnati ne da ya kunshi likitoci da masanan kimiya da ake kira “USPSTF” a takaice, wanda suka hada kai domin bada hanyoyin kariyar cututtuka da kuma yin gwaje-gwaje suka bada wannan shawarar.

Kwamitin USPSTF ya bayar da wannan shawarar ne a shekara ta 2005 tare da bukatar ganin ana gwada mutanen dake da hatsarin kamuwa da cutar.

Amma masana sun bada shawarar yin sauyin da zai karfafa yin gwajin a matsayin hanyar kariya dake karkashin wannan doka.

Dokar lafiya ta Shugaba Obama, ta bukaci masu gwajin su bi umurnin kwamitin. Yanzu dokar lafiya ta bada ikon yin gwaji ga kowanne mutum tsakanin shekara 15 zuwa 65, wadanda ke da hatsarin kamuwa da cutar.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG