Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Leken Asiri Na Majalisar Dattawan Amurka Ya Ce Rasha Ta Yi Shishigi A Zaben 2016 Na Shugaban Kasa


Shugaban Amurka Donald Trump

Kwamitin leken asiri na majalisar dattawan Amurka ya tabbatar cewa Rasha ta yi shishigi a zaben shugaban kasa na shekarar 2016 kuma ya taimakawa shugaba Trump

Shugaban kwamitin leken asiri na Majalisar Dattijan Amurka Richard Burr yace binciken da kwamitinsa yayi ya nuna shishigin Rasha a zaben shugaban kasar da aka yi a shekara ta dubu biyu da goma sha shidda domin taimakawa shugaba Trump lashe zaben.

Jiya Laraba shugaban kwamitin, wanda kuma dan jam’iyar Republican ne yayi wannan furuci. Yace babu dalilin da zai sa ayi tababan sakamakon binciken. Yace ko tantama babu Rasha tayi katsalanda a zaben da aka yi.

Mukadashin shugaban kwamitin Mark Warner dan jam’iyar Democrat ya yabawa aikin kwamitin. Yace shugaban Rasha Vladimir Putin da kan sa, ya bada umarnin kasar sa tayi shishigi a zaben da nufin taimakawa Donald Trump domin kada Hillary Clinton taci zabe.

Senata Burr yace kwamitin ya tantance haka ne bayan da wakilan kwamitin sun shafe watani goma sha hudu suna nazarin bayanai.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG