Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Nada Sarkin Gombe Ya Tantance Mutane 10


Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo
Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo

Kwamitin da gwamnati ta kafa domin ya samo sabon sarkin Gombe ya tantance sunayen mutane goma kuma tuni ya mikasu ga gwamnan jihar ya tabbatar da mutum daya.

Biyo bayan rasuwar sarkin Gombe gwamnatin jihar ta kafa kwamitin da zai tantance masu bukatar sarautar ya kuma ba gwamnati shawara.

Kwamitin da aka dorawa alhakin zakulo sabon sarki ya kammala aikinsa inda ya tantance sunaye goma ya kuma mikasu ga gwamnan jihar Ibrahim Hassan Dankwambo domin ya zabi mutum guda da za'a nada sarkin Gombe na goma sha daya.

Shugaban kwamitin Uban Doman Gombe Magaji Muazu yayi karin bayani akan aikinsu. Yace sun gama aikinsu. Yanzu komi na hannun gwamna. Abun da ya rage shi ne gwamna ya bincika abun da suka yi ya zabi wanda za'a ba sarautar. Yace mutane goma suka nema kuma sun bayar da nasu bayanin akan kowanesnu sun mikawa gwamna. Yace aikin tantancewar yana da sauki. Duk wadanda suka nema sun cancanta. Duk sun yi karatu. Sun yi aiki. Kwararru ne kuma.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammed.
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:36 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG