Bangarorin da ke rikici da juna a kasar Yemen sun taru a kasar Sweden, a wani sabon zangon tattaunawa kan yadda za a kawo karshen rikicin, wanda aka kwashe shekaru hudu ana yi.
Rahotanni sun nuna cewa rikicin na Yemen, na gab da jefa kasar cikin matsalar yunwa.
An fara tattaunawar ce a birnin Rimbo a ranar Alhamis, karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya.
Wanannan zaman sasanta rikicin, shi ne na farko ciki shekaru biyu, wanda ake yi tsakanin gwamnatin kasar ta Yemen mai samun goyon bayan Saudi Arabia, da kuma ‘yan tawayen Houthi da ke samun goyon bayan Iran.
Taron na gudana ne, a dai-dai lokacin da kasashen duniya ke suka, kan yadda al’umar kasar ta Yemen ta fada cikin wani hali, da kuma kisan dan jaridar kasar Saudiya Jamal Khashoggi.
Za ku iya son wannan ma
-
Afrilu 01, 2023
Ranar Talata Trump Zai Mika Kansa Ga Hukuma
-
Maris 29, 2023
Ukraine Ta Kaiwa Rasha Wani Mummunan Hari
-
Maris 29, 2023
Kasar Azerbaijan Ta kaddamar Da Binciken Harin 'Yan Ta'adda
Facebook Forum