Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Zata Kara Sojoji a Afirka Ta Tsakiya


Dakarun hadadiyar kungiyar Afirka masu kiyaye zaman lafiya a Afirka Ta Tsakiya

Sabili da rikicin Afirka Ta Tsakiya wanda har yanzu ya ki karewa, kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai kara tura sojoji domin a gaggauta kawo karshen rikicin.

Kwamitin Sulhun MDD na shirin bada izinin kara yawan wata sabuwar rundunar sojojin kiyaye zama lafiya a kasar jamahuriyar Afirka ta Tsakiya.

A yau Alhamis ake kyautata zaton cewa Kwamitin Sulhun zai zartas da kudirin na neman rundunar sojoji dubu 10 da 'yan sanda dubu daya da 800 domin su taimaka wajen farfado da bin doka a kasar wadda ruwan rikici ya ciwo.

A cikin daftarin kudirin da Rediyon Muryar Amurka ya samu ganowa, rundunar sojojin ta MDD za ta fara aiki a ranar 15 ga watan Satumba, idan ta karbi aikin daga hannun rundunar sojojin kasashen Afirkan da yanzu haka ke kasar jamahuriyar Afirka ta Tsakiya.

Sojojin dubu 6 na kasashen Afirka da dubu biyu na kasar Faransa sun kasa shawo kan rikicin addinin da ya lankwame rayukan dubban mutane.

A jiya Laraba hukumomin kasar da shaidu sun gayawa Sashen Faransanci na Muryar Amurka cewa an kashe mutane 30 a kalla bayan da mayakan anti-balaka su ka kaddamar da wani hari a garin Dekoa a yankin tsakiyar kasar. Akasarin wadanda harin ya rutsa da su fararen hula ne.

Hukumomi da shaidu sun ce da halama bisa kuskure mayakan anti-balaka suka farma fararen hular, a zaton su 'yan tawayen Seleka ne wadanda akasarin su Musulmi ne.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG