Ana sa ran babban jami'in kula da harkokin siyasa na majalisar, Jeffrey Feltman shine zai yiwa kwamitin jawabi a wajajen rana yau Laraba.
Wannan mataki ya biyo bayan kudurin da kwamitin sulhun ya zartas jiya Talata,inda ya bukaci duka sassan da suke rikici, su kare asibitoci, da masu aikin kiwon lafiya, da cibiyoyin kiwon lafiya daga tarzoma, kuma za'a ladabtar ko aza laifi kan duk wanda yaki bin wannan umarni.
Matakin na kwamitin sulhu ya zama wajibi ganin munanan hare hare da ake kaiwa kan asibitoci a wurare da ake fama da fadace-fadace a fadin duniya.
A wasu hare hare da jiragen yakin Syria suka kaddamar har sau 30 ranar Asabar data wuce, a bangaren birnin Aleppo da yake hannun 'yan tawaye ya kashe akalla mutrane biyar. Wani roka da 'yan tawaye suka harba jiya Talata, ya farwa wani asibiti a Aleppon, ya kashe akalla mutane 3.