Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Sulhu Ya Kira Bangarorin Dake Fafatawa Da Juna A Syria Su Bi Umurnin MDD


Motocin dake kai agaji Syria
Motocin dake kai agaji Syria

Shugaban Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, MDD, a wani zaman kwamitin jiya Laraba Karel Van Oasterom ya bukaci duka bangarorin da suke fafatawa da juna a Syria su bi umurnin MDD.

Shugaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, MDD, Karel Van Oasterom ya jaddada kiran da majalisar tayi na neman dukkan bangarorin Syria su aiwatar da umarnin tsagaita wuta, ya kuma bayyana damuwa dangane da halin kunci da al’umma ke ciki a Syria.

Van Oasterom ya bayyana haka ne bayan wani zaman kwamitin sulhun jiya laraba domin tattaunawa kan shirin tsagaita wuta na kwanaki 30 da kwamitin sulhun ya bukaci a aiwatar cikin wani kuduri makonni biyu da suka shige, wanda kuma aka yi watsi da shi.

Rashin kiyaye kudurin tsagaita wutar ya sa Birtaniya da Faransa suka bukaci yin wannan zaman sirri na kwamitin sulhu.

An ci gaba da gwabza kazamin fada jiya laraba a gabashin Ghouta, yankin da ya kasance tungar ‘yan tawaye a wajen babban birnin kasar Syria, wanda kuma tun a shekarar 2013 dakarun gwamnati suke kai masa farmaki. Dakarun gwamnati sun yi ta luguden wuta a yankin da jiragen sama suka kashe daruruwan mutane. Hare haren da gwamnatin kasar ta fara kaiwa makonni biyu da suka shige a yankin da yake daya daga cikin wurare na karshe dake hannun ‘yan tawaye a kusa da Damascus, ya kasance daya daga cikin kazaman hare hare da aka kai tunda aka fara yakin kusan shekaru takwas da suka shige.

Kungiyar kare hakkin bil’adama dake sa ido kan harkokin Syria ta sanar jiya cewa, hare haren da gwamnatin Syria ke kaiwa sun raba Ghouta gida biyu,da cewa, a yanzu sojojin gwamnati na iya yin harbi a kan kusan kowane bangare na wani dan zirin da ya hada bangaren arewaci da kudancin Ghouta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG