Accessibility links

Kwamitin Sulhu Zai Fadada Wakilai Masu Sa Ido A Rikicin Syria

  • Aliyu Imam

Mazu zanga-zanga suke rike da wani zanen hoton Shugaba Assad, bayan sallar jumma'a a wani gari kusa da Homs.

Kwamitin sulhu na MDD ya cimma daidaito kan kudurind a zai bada ikon fadada wakilai masu sa ido kan shirin tsagaiata wuta a Syria daga 30 zuwa 300.

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya cimma daidaito kan kudurind a zai bada ikon fadada wakilai masu sa ido kan shirin tsagaiata wuta a Syria daga 30 zuwa 300.

Jakadan faransa a Majalisar, Gerard Araud, yace yau Asabar kwamitin zai zauna domin kada kuri’a.

Matakinda Majalisar ta daukan yazo ne a dai dai lokacinda shirin tsagaita wuta da aka cimma makon jiya, karkashin jagorancin wakilin kasa da kasa kofi Annan, yake kara nuna alamun rugujewa a wunin jiya jumma’a.

An bada labarin jami’an tsaro sunyin harbi kan masu zanga zanga, kuma sukayi luguden wuta kan tungayen ‘yan hamayya. Ita kuma gwamnati tana zargin ‘yan tawaye da haddasa wata mummunar fashewa.

‘Yan gwagwarmaya suka ce dubun dubatan masu zanga zanga dake kiran shugaba Bashar al-Assad yayi murabus ne suka yi gangami a duk fadin kasar, an baza jami’an tsaro sosai a wuraren zanga-zangar.

XS
SM
MD
LG