Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitocin Majalisar Wakilan Amurka Sun Zargi Pompeo Da Taurin Kai


Shugabannin wasu kwamitocin majalisar wakilan Amurka uku masu karfin fada-a-ji, sun zargi Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, “da nuna fifiko” ga abin da zai amfane shi, a binciken da ake yi kan shugaban Amurka Donald Trump, binciken da mai yiwuwa ya kai ga tsige shi.

Pompeo na kokarin ya hana wasu tsoffin jami’an ma’aikatar harkokin wajen Amurka da wasu da ke aiki a ma’aikatar a yanzu zuwa ba da shaida, wanda wani mataki ne da ake so a dauka a fara binciken shugaban na Amurka.

Sai dai a yammcin jiya Talata, shugabannin kwamitocin harkokin wajen Amurkan, da na tattara bayanan sirri da kuma na wanda ke kula da kwamitocin majalisar wakilan kasar, sun ce, idan dai har abin da rahotanni ke nunawa da gaske ne Pompeo ya saurari hirar da Shugaba Trump ya yi da takwaran aikinsa na Ukraine Volodymyr Zelenskiy a ranar 25 ga watan Yuli, hakan na nufin Pompeo ya zama shaida.

Shugabannin kwamitocin sun kuma gargade shi da ya guji daukan wani mataki kan wanda zai ba da shaida ko kan wasu takardu a wani mataki na kokarin kare kansa.

A nasa bangaren, Pompeo ya zargi ‘yan majalisar ta wakilai na bangaren Democrat, da yunkurin yin barazana ga jami’an ma’aikatar harkokin wajen Amurkan su biyar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG