Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwankwaso Ya Kaddamar Da Cibiyar Kula Da Wadanda Suka Tuba Daga Tu’ammali Da Miyagun Kwayoyi A Kano


Kwankwaso
Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan majalisa mai wakiltar mazabar Kano ta tsakiya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kaddamar da cibiyar Amana Sanatorium mai kula da mutanen da suka yi tu’amali da miyagun kwayoyi a baya a jihar Kano.

Sanata Kwankwaso ya kaddamar da cibiyar ne a yayin murnar cikarsa shekaru 65 a duniya.

Cibiyar da zata amafane jama’a ta fanonni daban-daban wacce ke a kauyen Jido da ke karamar hukumar Kano municipal a kan babbar hanyar Kano zuwa Wudil na da sashen kula da masu fama da matsanancin damuwa da gyara hali.

Da yake jawabi a wajen kaddamar da cibiyar, Sanata Kwankwaso ya ce an kafa cibiyar gyarar al’umma ne saboda mutanen da ke ko kuma suna fama da matsalar tu’amali da miyagun kwayoyi wadanda ke bukatar kulawa na musamman su dawo daidai.

A cewar Kwankwaso, a baya gwamnatin tarayya da na jihohi sun samar da cibiyoyin gyara da aikin gudanar da su amma daga baya aka yi watsi da wadannan cibiyoyin da ke taimakon al’umma.

Haka kuma, Kwankwaso ya ce a cibiyar, wadanda ke fama da matsalar yin maye za su sami kulawan kwararrun likitocin a fannin kula da masu fama da matsanancin damuwa da tabin hankali, ma'aikatan jinya, kwararrun likitocin asibiti, masana zamantakewa, masu ilimin kula da kwakwalwa, masu ba da shawara da masu koyar da addini, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Za’a kuma yi wa mutanen da ke da fama da ciwo mai alaka da sakamakon tu’amali da miyagun kwayoyi a cibiyar don ba su damar sake komawa rayuwarsu ta yau da kullun, in ji shi.

XS
SM
MD
LG