Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwayar Cutar Da Ta Bullo a China Ka Iya Yaduwa Cikin Sauri - Masani


Wani masani a China ya yi kashedi cewa muguwar kwayar cutar nan da ta bullo daga birnin Wuham ka iya samun karfi da za ta kara saurin yaduwa daga wannan zuwa waccan.

Wannan kwayar cuta mai suna corona virus mai kama da hakarkari na nimoniya ta addabi kusan mutane dubu uku a fadin duniya kana ta kashe mutane 56 a China, lamarin da ya sa gwamnatoci suka bullo da matakan kare ‘yan kasar su.

‘Yan kasar China mazauna Faransa sun yi bukin cika shekarar Sinawa a ranar Asabar cikin alhini, ya yin da suke shiga sabuwar shekara. Duk da damuwar bazuwar wannan mummunar kwayar cuta a China, mahalartan taron faretin sun yi raye raye a kan tituna gunduma ta takwas a Paris.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG