Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kyari Ya Taimaka Wajen Maido Da Kudaden Abacha – Amurka


Marigayi Abba Kyari

Gwamnatin Amurka ta kwatanta Shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayyar Najeriya, marigayi Mallam Abba Kyari a matsayin jajirtaccen ma’aikaci wanda take “girmamawa.”

Wata sanarwa da ta fito daga hannun kakakin Shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu a ranar Juma'a, wacce VOA ta samu, ta nuna cewa, gwamnatin Amurkan ta yabi marigayin ne a wani sakon ta’aziyya da ta aike ta hannun mataimakin sakataren harkokin wajen kasar mai kula da nahiyar Afirka, Tibor Nagy.

A cikin sakon ta’aziyyar a cewar sanarwar ta Shehu, Nagy ya ce marigayi Kyari “ya taka muhimmiyar rawa wajen karbo dala miliyan 300 da tsohon shugaban Najeriya Sani Abacha ya sace.”

“Kyari, ya kasance mutum mai muhimmanci a gare mu da kuma zama mai shiga tsakani ga gwamnatin Amurka, musamman ga tawagarmu da ke Abuja.” In ji Nagy, kamar yadda sanarwar ta nuna.

“Mun ji dadin aiki da shi kan muhimman batutuwa da dama, ciki har da taimaka wa wajen maido da kudaden al’umar Najeriya dala miliyan 300 da gwamnatin Abacha ta sace.”

A dai ranar Juma’ar da ta gabata, Kyari ya rasu bayan fama da ya yi da cutar coronavirus na tsawon makonni.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG