Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

LABARAN WASANNI A TAKAICE: Kofin Zakarun Turai Da Sauran Wasanni


David Alaba, défenseur autrichien du Bayern, lève les mains à la victoire de son équipe contre Besiktas au parc de Besiktas à Istanbul, 14 mars 2018.

Za mu soma labarun wassaninmu na yau da kofin zakarun Turai na kwallon kafa da a ke kira Champions ligue, inda ake can ake karawa ta 2 a Spain, tsakanin Villareal dake rike da kofin Europe Ligue wadda kuma ta kai a wannan matsayin na kusa da na karshe wadda ake kira Semi - Finale ko demi Finale a Turance, na Champions ligue din na bana, bayan ta gwabcike Bayern Munich ta kasar Jamus a zagayen kar de Finale ko kwatafainal (1/4 Finale) da a daya hannun, Liverpool tayi mata 2 – 0, mako guda da ya gabata a kasar Ingila.

Wasan na 2 na wannan kombalar ta bana, a wannan matsayin na kusa da na karshe, zai wakana gobe a kasar Spain Tsakanin Real de Madrid da Man - City.

Kungiyoyin guda 2, sun kara a Ingila mako guda da ya gabata, inda Man City ta yi nasara da ci 4 - 3.

Gameda da ma wasan na gobe tsakanin Real de Madrid da Man City, dan wasan club din na Real de Madrid, David Alaba, ba zai samu damar buga wasan na gobe ba, idan Allah ya kaimu, kasancewar a yau Talata, bai samu damar bullowa ba a wurin atisaye.

Shi dai David Alaba dan Kasar Australiya da ke buga wa club din na Real de Madrid, na fama da ciwo a damtsen sa, kuma bisa ga dukkan alamu, ana iya cewa har yanzu, jijiyoyinsa ba su sake ba, balle ya buga tamola.

Shi ko shugaban kungiyar kwallon kafa ta Olympique de Marseille ta kasar Faransa, yanzu haka, ya na ta kai gwauro ya na kai mari, domin ganin kocin kungiyar, Jorge Sampaoli, ya kara rattaba hannu a kan kwantaraginsa domin ya tsaya bayan ma shekara ta 2023, shekarar yarjejeniyar da ke gare shi da kungiyar a halin yanzu ke karewa.

Jorge Sampaoli, ya tado da komadar kungiyar ta Olympique de Marseille da ta taba lashe kofin zakarun Turai na kwallon kafa a 1993. Tun kama ragamar kungiyar ta OM a bara, cocin mai zafin nama, ya kai ta yanzu haka a matsayi na 2 a alkaluman kakar kwallon kafa ta bana, kuma za ta buga wasan kusan da na karshe na 2 a gobe da Feyonoord Rotermad, da ta yi mata 3 - 2 mako guda da ya gabata a kasar Holland.

Idan muka leka fagen wasanin Conference Est na kwallon kwando na kasar Amurka kuwa, kungiyar Miami ta sha Philadelphia da ci 106 da 92 a wasan kungiyoyin na 2.

A wannan gasar, kungiyar tayi ci 4 daga cikin wasannin da za ayi a nan gaba ita ce zata kai ga zagaye na gaba.

Duk dai a wannan kombalar ta wasanin kwallon kwando na Conference Ouest na kasar Amurka, Golden States dakiyar da sudin goshi sun wa Memphis ci 117 - 116 a karon su na farko daga cikin neman nassarori 4 ga kowace kungiya domin kai ga wasanni na gaba na wannan kombalar ta bana.

Saurari rahoton Haruna Bako:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

Dubi ra’ayoyi

AFCON 2021, Troost-Ekong

Abin da kyaftin Troost-Ekong ya ce da Najeriya ta lashe wasanninta uku a jere bayan doke Guinea-Bissau
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:15 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021, Super Eagles

Yan wasan Najeriya na atisaye gabanin karawar da za su yi da Guinea-Bissau a rukunkin D na gasar AFCON
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:08 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021: Troost-Ekong

Kowa ya san cewa mun iya taka leda’ In ji Troost-Ekong, yayin da Najeriya ta kai zagayen knockouts
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:03 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021, Kelechi Iheanacho

"Ku doke daya daga cikin shahararrun koci a duniya", Kelechi Iheanacho, Najeriya bayan sun doke Masar
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:11 0:00
Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG