Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Laberiya Zata Tusa kayar Wasu 'Yan Kasar Ivory Coast Zuwa Gida Domin....


Shugaban Amurka Barack Obama da wasu shugabannin Afirka ciki har da Allassane Ouattara na Ivory Coast.

Jami’ai a kasar Liberia sun ce Gwamnati na shirin sake maida ‘yan kasar Ivory Coast 41 dake gudun mafaka zuwa gida domin su fuskanci hukunci kan zargin.

Jami’ai a kasar Liberia sun ce Gwamnati na shirin sake maida ‘yan kasar Ivory Coast 41 dake gudun mafaka zuwa gida domin su fuskanci hukunci kan zargin hannun da suke dashi na tada hargitsin siyasar bayan kammala zabe a kasar Ivory Coast.

Sai dai Liberia tayi kukan da nuna damuwa kan gujewar da wasu giggain magoya bayan hambararen shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo, domin har yanzu ba’a san inda suka shiga ba.

Tsohon shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo yanzu haka yana fuskantar shari’a a kotun kasa da kasa dake birnin Hague ana tuhumarsa da laifin cin mutunci da wulakanta Bil Adama. Yasha akaye a babban zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Nuwamaban shekarar 2010 a Ivory Coast, amma yaki sauka daga mulki, hakan ne kuma ya janyo tada zaune tsayen da har mutane sama da dubu uku suka halaka.

Mayakan Bangar tsohon shugaba Gbagbo da sojin hayar Liberia dake mara masa bayan suna samun mafaka a yankin kan iyakar gabashin Liberia.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG