Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lalata da Mata A Sansanin 'Yan Gudun Hijra A Arewa Maso Gabashin Najeriya


Wasu cikin 'yan gudun hijira dake jihar Borno
Wasu cikin 'yan gudun hijira dake jihar Borno

Rahoton hukumar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch ya bayyana yadda ake cin zarafin mata ta yin lalata dasu ta hanyar fin karfinsu a sansanin 'yan gudun hijira a arewa maso gabashin Najeriya.

Irin wannan hanyar cin zarafin matan ya kara nuna halin takaici da 'yan gudun hijiran suke ciki baicin batun rashin wadatar abinci.

Tuni dai shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya bada umurnin binciken gaskiyar rahoton domin daukan matakin da ya dace.

Mai taimakawa shugaba Buhari kan labaru Garba Shehu yayi karin bayani. Yace da rahoton ya kai garesu shugaban kasa ya nuna damuwarsa tare da bacin rai cewa mata da suka fi rauni da suke zaune a sansanin 'yan gudun hijira a ce har ana zaluntarsu, yace gwamnatinsa ba zata lamunta da irin hakan ba.

Shugaba Buhari ya umurci 'yansanda da shugabannin jihohin Adamawa da Borno da Yobe su bincika lamarin su kawo masa rahoto kafin ya san matakin da zai dauka.

Su gwamnonin na arewa maso gabas da suke da 'yan gudun hijira na kokarin maidasu garuruwansu ko kuma wuraren da suka dace domin rufe sansanonin. Da ma can tsohuwar mai kula da 'yan gudun hijira ta Najeriya Hajiya Sani Kangiwa ta dade tana jan hankali kan wannan lamarin.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:47 0:00

XS
SM
MD
LG