Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lamarin Jin 'Kai a Siriya Na Ci Gaba Da Kazancewa - MDD


Majalisar Dinkin Duniya ta ce halin da ake ciki a Siriya na dada kazancewa, kuma miliyoyin mutane na ci gaba da fama da karancin kayan jinkai a fadin kasar.

Aikin wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman a Siriya Najat Rochdi shi ne kula da halin jinkai da ake ciki a kasar. Ta ce halin da ake ciki a wannan kasar, wadda ta shafe shekaru sama da 8 ta na gwabza yaki, na da ban tsaro. Ta na mai kira ga al’ummar duniya da ta kare tare da tallafa ma farar hulan da ke fuskantar barazana, wadanda ba su ma da dan kayan masarufin da zai raya su.

Ta ke mutane kimanin miliyan 11.7 na bukatar tallafin kayan jinkai kuma wajen miliyan biyar na cikin tsananin rashi. Ta ce abin ya ma fi muni ga wasu farar hulan da su ka kwashe wata guda a tsakiyar musayar wutar da aka yi ta yi tsakanin sojojin gwamnati da dakarun ‘yan tawaye a yankin Idlib da ke arewa maso yammacin Siriya.

Mai maganata da yawunta, Jenifer Fenton, ta ce farar hula a kalla 350 aka kashe sannan kuma wasu sama da 330,000 sun rasa muhallansu. Ta ce wasu mutane kimanin miliyan 3 na fuskantar takamaiman hadari. Ta ce sun makale a yankin da ake tafka yaki don haka makomarsu na ga Allah, na ga bangarori biyun da ke gwabza yaki saboda babu ta yadda za su tsiri.

“Ana ci gaba da lalatawa da kuma ruguza madafun rayuwa. Babban abin da ke gabanmu shi ne kare farar hula. Farar hula masu yawan gaske na ta mutuwa. Yakar ‘yan ta’adda mai zama uzuri ga kowa na ya kasa sauke nauyin da ya rataya a wuyarsa a matakin dokar kasa da kasa ba, kuma mu na masu cigaba da kiran dukkan bangarorin da su mutunta yarjajjeniyar da aka cimma don a kawo kwanciyar hankali.”

Fenton ta ce al’amarin na ci gaba da fin karfin mutane wajen 70,000 da ke zama a sansanin Al Hol mai cike da kazanta da kuma cinkoso a arewa maso gabashin Siriya. Waddannan mutanen sun gudu ne zuwa Al Hol tun bayan da gwamnatin Siriya ta kwace Deir-Ez-Zour, wuri na karshe da ya rage a hannun tsattsaurar kungiyar nan ta ISIS.

Akasarin mutanen da ke wannan sansanin mata da yara ne ‘yan asalin Siriya da Iraki. Mutanen na kunshe da iyalai wajen 11,000 da ake zargin na mayakan ISIS ne daga kasashe da dama. Kasashensu na jan kafa wajen dawowa da su saboda hukunta mayakan ISIS zai kasance mawuyacin abu gare su kuma zai hada su rigima da ‘yan kasa.

Asusun Kula Da Yara na MDD da sauran cibiyoyi na kira ga kasashe da su maida mutanensu gida wadanda su ka hada da yara kimanin 29,000 da mayakan ISIS su ka haifa, sun a masu jaddada cewa yaran basu da laifin komai, hasali ma su wahal da su aka yi a wannan mummunan yaki.

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya Mai Kula da Harkokin Jinkai ya ba da rahoton kwasar wasu yara zuwa kasashensu a cikin ‘yan makwannin da su ka gabata. To amma ofishin ya kara da cewa har yanzu akwai wasu dubbai a Al Hol, kuma su na fuskantar makoma marar tabbas.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG