Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lambar Yabo Ta Zaman Lafiya Nobel Peace Prize


Kaci Kullmann Five, head of the Norwegian Nobel Committee, announces the winner of 2015 Nobel peace prize during a press conference in Oslo, Norway, Oct. 9, 2015.

An bada lambar yabo ta Nobel, ta zaman Lafiya na wannan Shekarar ta 2015, ga wata cibiyar kungiyoyi guda hudu na kasar Tunisiya.

An jinjinawa kungiyoyin ne dai saboda taimakon da suka bada wajen shimfida akidar dimokaradiyya a kasar, bayan juyin juya-halin Jamine da akayi na shekarar 2014.

A yau Juma'a ne kwamitin bada kyautar Nobel ya bada sanarwar a birnin Oslo, na kasar Norway. Da cewa an bayar da kyautar ne ga kungiyoyi hudu a hade, ba'a rarrabe su ba, saboda namijin kokari da sukayi na raya dimokaradiyya bayan tashe tashen hankalin da suka faru a kasashen larabawa, wanda ya hada da kashe kashen siyasa da makamantansu.

Kwamitin ya yaba wa kungiyoyin saboda aikin da suka yi na ceto kasar ta Tunisiya, daga abkawa cikin yakin basasa gadan gadan.

XS
SM
MD
LG