Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lamidon Adamawa Ya Kira A Duba Rahoton Taron Kasa da Suka Yi


Barkindo Aliyu Mustapha Lamidon Adamawa

Lamidon Adamawa ya kira a duba rahoton taron kasa da suka yi lokacin gwamnatin da ta shude za'a lalubo bakin zaren matsalar sake fasalin Najeriya

Mai martaba Lamidon Adamawa Dr. Mohammadu Barkindo Aliyu Mustapha, ya yi kira ga gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta yi nazari kan rahoton 'taron kasa' da gwamnatin data shude ta Godluck Jonathan ta kaddamar da nufin aiki da shawarwari da taron ya bayar.

Lamidon wanda yana daga cikin wadanda suka daga muriya lokacin taron, yace aiki da shawarwarin kwamitin zai shawo kan dukkan kiraye kirayen da ake yi yanzu na neman sake fasalin Najeriya, domin babu wani bangare na kasar da bai sami wakilci a taron ba.

Lamidon Adamawa wanda yazo Abuja karkashin laimar sarakunan gargajiya na Najeriya wadanda suka zo taya shugaba Buhari murnar dawowa gida lafiya daga jinyar da yayi a Ingila, yace kodayake masu kiraye kirayen a sakewa kasa fasali basu fayyace ainihin baudin da suke so ba, duk da haka yayi tur da masu neman a koma bin tafarkin bangaranci wadda Najeriya ta gwada a zamanin jamhuriya ta farko.

Shi dai Lamidon Adamawa yana cikin masu goyon bayan a kafa rundunar 'Yansanda a kananan hukumomi da kuma jihohi. A ganinsa wannan yana daga cikin tsarin sake fasalin Najeriya.

Ya shawarci gwamnatin Buhai ta hanzar ta yi nazarin rahoton kwamitin da ya ce yana kunshe da kyawawan shawarwari da zasu taimaka wajen kwantarwa jama'a zukatu a dai dai lokacin da kasar ta goce da neman a sake fasalin kasar.

Ga firar da Sahabo Imam Aliyu ya yi da Lamidon.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:37 0:00

Facebook Forum

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG