Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Laraba Za'a Fara Taron Kasa Da Kasa Kan Libya A Qatar


Hayaki yake tashi kusa da wata hanya a Libya,inda har yanzu ake fafatawa.

Jami’an diflomasiyya sun shirya domin ganawa yau laraba a Qatar da nufin tsara matakan da duniya zata dauka game da rikicin Libya, a yayin da faransa da Britaniya suka bukaci kungiyar kawancen tsaron NATO da ta zafafa hare-haren da take kaiwa daga sama a kan sojojin gwamnati

Jami’an diflomasiyya sun shirya domin ganawa yau laraba a Qatar da nufin tsara matakan da duniya zata dauka game da rikicin Libya, a yayin da faransa da Britaniya suka bukaci kungiyar kawancen tsaron NATO da ta zafafa hare-haren da take kaiwa daga sama a kan sojojin gwamnati da suka ce su na kai farmaki kan fararen hula.

Wannan Kungiyar Tuntubar Juna Kan Libya,wadda zata yi taronta na farko, zata hada hancin kasashen yammaci da na yankin wadanda suka bayyana goyon bayansu ga ‘yan adawar kasar Libya.

Majalisar Mulkin Wucin Gadi ta Kasa da ‘yan tawaye suka kafa ta ce zata tura tawaga, haka shi ma babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon, yace zai halarci taron.

Tsohon ministan harkokin wajen Libya, Moussa koussa, wanda ya canja sheka ya koma Britaniya yace zai halarci taron a matsayin mai bayar da shawara. Jiya talata, ministan harkokin wajen faransa, Alain Juppe, yace NATO ba ta daukar kwararan matakan da suka kamata domin hana mayakan shugaba Muammar Gaddafi kashe fararen hula a yankunan dake hannun ‘yan tawaye. Yace tilas kungiyar ta dauki karin matakan lalata manyan makaman Mr. Gaddafi da ake amfani da su kan birnin Misrata na yammacin kasar.

Kungiyoyin agaji na duniya su na kashedin cewa za a fuskanci bala’I na jinkai a birnin na uku wajen girma a Libya. Ministan tsaron Faransa, Gerard Longuet, yace idan ba har Amurka ce ta shiga cikin wannan yunkuri baki daya ba, tana yiwuwa NATO ba zata iya hana mayakan Gaddafi kai farmaki kan biranen dake hannun ‘yan tawaye ba.

Jami’an Amurka sun fada jiya talata cewa ba su da wani shiri na kara tsoma hannun sojojin Amurka a wannan sha’ani na Libya, kuma NATO ma ba ta nemi Amurka da ta yi hakan ba.

NATO ta yi watsi da sukar da kasashen Faransa da Britaniya suke yi. Birgediya Janar Mark Van Uhm ya fada jiya talata cewa NATO tana gudanar da gagarumin aiki abin yabo, tana kuma kare fararen hula da irin albarkatun dake hannunta.

XS
SM
MD
LG