Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa da Ingila sun bukaci kungiyar tsaro data NATO ta kare farar hula a Libya.


Mayakan 'yan tawayen Libya.

Kasashen Fasansa da Ingila sunyi kira ga kungiyar kawancen tsaro ta NATO data kara daukan matakan kare farar hula a Libya. Kasashen sunyi wannan kira ne a yayinda fada ya zafafa tsakanin sojojin gwamnati dana 'yan tawaye bayan da shirin tsagaita bude wuta ya rargaje. To amma Ministan harkokin wajen Faransa ya fada Talatan nan cewa tilas sojojin kawance su kara zage dantse domin lalata manyan makaman shugaba Moammar Gaddafi na Libya.

Kasashen Fasansa da Britaniya sun bukaci kungiyar kawancen tsaro ta NATO data dauki karin matakan kare farar hula a kasar libya. Kasashen biyu sunyi wannan kira ne a yayinda fada ya munance tsakanin sojojin gwamnati da yan tawaye bayan wargajewar shirin tsagaita bude wuta. Kungiyar NATO tana ta kai hare hare da jiragen saman yaki a yayinda take kokarin ganin cewa jiragen sama basa shwagi a sararin samaniyar kasar. To amma Ministan harkokin wajen Faransa Alain Juppe ya fadawa gidan rediyon Faransa talatan nan cewa tilas sojojin kawancen kungiyar NATO su kara zage dantse domin lalata manyan makaman shugaba Moammar Gaddafi. Mr Jupe yace zai tado wannan batu a lokacin taron ministocin harkokin wajen kungiyar kasashen turai a yau talata da kuma na Ministocin NATO da za'a yi a wannan makon idan Allah ya yarda. Ganaral Mark Van Uhm na kungiyar NATO ya fadawa kamfanin dilancin labarun Associated Press cewa yana gani sojojin kawance suna rawar gani bisa la'akari da kayayyakin aikin da suke dasu. Shi kuma sakataren harkokin wajen Ingila William Hague yayi kira ga kasashen kungiyar nATO da su kara yawan jiragen saman yaki kamar yadda Ingila tayi. An zatar da kudurin hana shawagin jiragen sama da nufin kare farar hula daga hare haren da sojojin Gaddafi ke kaiwa. A yau talata sojojin gwamnati suka yiwa birnin Misrata wanda ke hannun yan tawaye luguden wuta.

XS
SM
MD
LG