Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Larabawa Sun Musanta Zargin Yiwa Zaben Amurka Na 2016 Shishigi


Ministan harkokin wajen Saudiyya Adel al-Jubeir
Ministan harkokin wajen Saudiyya Adel al-Jubeir

Biyo bayan labaran da wasu kafofin kafofi suke yayatawa na cewa dan shugaban Amurka ya gana da shugabannin Larabawa gabanin zaben 2016 ya sa Larabawa suka fito fili suka musanta batun

Hadaddiyar Daular kasashen Larabawa ta ce ba ta yi yinkurin yin katsalandan a zaben Shugaban Kasar Amurka na 2016 don amfanar Donald Trump ba.

Ministan Harkokin Wajen Hadaddiyar Daular kasashen Larabawa Anwar Gargash ya karyata hakan ta kafar ‘twitter’ jiya Talata bayan da kafafen yada labarai a Amurka su ka ruwaito cewa dan Trump ya gana da Jakadun Saudiyya da Hadaddiyar Daular kasashen Larabawa a 2016.

“Ya kamata a fuskanci gaskiya a maimakon gugar zana da kuma yada jita-jita. Hadaddiyar Daular Larabawa ba ta yi yinkurin yin katsalandan a zaben Shugaban kasar Amurka na 2016 ba,” a cewar Gargash. Ya kara da cewa, “Kamar sauran gwamnatocin da ke dasawa da Amurka, jami’an Hadaddiyar Daular kasashen Larabawa sun tattauna da jami’an yakin neman zaben bangarorin biyu a 2016, don su san inda kowane dan takara ya dosa game da manufofin kasashen waje.”

Jaridar New York Times ta ruwaito a makon jiya cewa dan Trump ya yi wata ganawar da ta kunshi wakilan Hadaddiyar Daular kasashen Larabawa da Saudiyya. An ce wai wani dan aike ya gaya ma dan Trump cewa a shirye Shugabannin kasashen biyu na Larabawa su ke su taimaka ma mahaifinsa ya ci zabe.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG