Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pakistan Ta Karyata Batun Mika Wa Amurka Likitan Da Ya Taimakamata Kashe Osama Bin Laden


Osama Bin Laden, shugaban al-Qaida wanda Amurka ta kashe a garin Abbottabad dake kasar Pakistan

Pakistan ta musanta batun tattaunawar sirri domin mikawa Amurka Afridi, liktan da ya taimaka wajen kashe Osama Bin Laden

Kasar Pakistan ta karyata wani rahoton da aka yayata jiya Alhamis da ke cewa wai kasart tana wata tattaunawar sirri domi ta mika wani likitan da yanzu haka yake hannu wanda shune ya taimakawa hukumar liken asirin kasar Amurka CIA ta samu nasarar kaiwa ga shugaban Al’kaida Osama Bin Laden sumame a shekarar 2011 kuma harma ta kashe shi.

Shakil Afridi dai shine likitan nan dan kasar Pakistan da ya jagoranci wani kanfen din karya na bada rigakafin cutar hanta inda ya samu kwayayen halitta na gado na iyalan gidan Bin Laden.

Wannan yunkurin ne ya taimaka ma sojojin kasar Amurka samun damar datse shugaban ‘yan ta’addan a garin Abbottabad dake tsakiyar kasar ta Pakistan.

Sai dai kwanaki kadan da aukuwar haka ne aka kame Afridi,bayan labarin ya bazu cikin duniya na irin rawar da ya taka na samamen da sojojin Amurka suka kai, abinda mahukuntar kasarPakistan suka yi ALLAH waddarai dashi suna cewa wannan ya karya diyaucin sun a kasa cikakkiya mai ‘yancin ci gashin kai.

Sai dai an gurfanad da wanna likitan gaban sharia kuma aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 23 na yi wadan taadda magani tare dataimaka masa da kudi a wata gunduma dake bakin iyakar kasar Afghanistan.

Sai dai mai Magana da yawun maaikatar harkoki kasashen waje Mohammed Faisal ya fada a wurin taron manema labarai cewa ba wata yarjejeniya tsakanin Pakistan da Amurka akan wannan batu.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG