Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lauyoyi Sunce Haramta Kungiyar IPOB Yayi Daidai.


Prince Ozo Onna ya shiga zanga zangar da akeyi kan shugaban Biafra Nnamdi Kanu.
Prince Ozo Onna ya shiga zanga zangar da akeyi kan shugaban Biafra Nnamdi Kanu.

Wasu Lauyoiyi da masana harkokin tsaro a Nigeria sunce haramta kugiyar nan mai rajin kafa jamhuriyar Biafra yayi dai-daui da abinda dokar kasa ta tanada

Kungiyar fafitikar kafa kasar Biafra bata da banbanci da kungiyar Boko Haram, don haka haramta ta yayi dai-dai, a cewar wasu lauyoyi.

Wani lauya mai zaman kansa Ibrahim Tukur El-Sudi ya shaidawa Hassan Maina Kaina cewa tunda kungiyar ta kama hanyar fito na fito da mahukuntar kasar, wannan yasa gwamnonin jihohin kudu maso gabas suka haramta ta.

Yace abinda wannan haramcin ke nufi shine dukkan abubuwa da suke yi tilas ne su daina idan ba haka ba ko sun karya doka kuma ana iya hukunta su.

Lauyan yace da zaran an kira wani da aikata ta’adanci, wato mutumin yana yin wasu abubuwan dake tsoratar da mutane, to bai kamata a barshi yaci gaba da wannan akidar ba.

Shima Aliko El-Rashid Haruna masanin harkokin tsaro cewa yayi wannan ayyanawar da ma’aikatar tsaro tayi na kiran kungiyar IPOB ta ‘yan taaada daidai ne.

Hassan Maina Kaina na dauke da karin bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:47 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG