Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lauyoyin Donald Trump Sun Nemi Alkali Ya Jinkirta Shari'a Sai Trump Ya Dare Mulki


Wani alkali a nan Amurka ya shawarci zababben shugaban kasa da ya tabbatar ya kammala shara’ar almundahanar dake gaban sa na game jami’ar sa.

Lauyoyin Trump sun tafi kotu a jiya Alhamis suna neman a jinkirta sauraron karar da aka shirya yi daga ranar 28 ga wannan watan, game da karar jami'ar Trump dake Califonia.

Lauyoyin suna neman a dage sauraren karar ce har sai an kammala rantsad da shi Trump ya fara aiki.

Lauyoyin suka ce wanda suke karewar bazai samu wadataccen lokacin halartar zaman kotun ba domin aiki zaiyi masa yawa a dai-dai lokacin mika mulki.

Mai shara'a Gonzalo Curiel ya shaida wa gungun lauyoyin cewa baida hurumin jinkirta karar amma zai bayyana shi a farfajiyar kotun a sati mai zuwa, sai dai kuma ya shawarci lauyoyin bangarorin biyu da su Tattauna tsakanin su domin cimma matsaya.

Daliban jamia'ar ta Trump da suka biya dala dubu 20 domin koyon darasin muhimmam dabarun saka hannun jari ga harkokin gidajen shi Trump din amma kuma suka ce an shara musu karya cewa shi Trump da kansa ne zai zabi wadanda zasu bada karatu a wannan kwas din.

Bayanan da aka gabatar gaban kotu ya nuna cewa an yaudari wadanda suka yi rajistan yin wannan kwas din kuma daga bisani ma aka yi biris da bukatun su ba tare da kula da yadda suke ji ba game da wannan karyar da aka yi musu.

Sai lauoyin na Trump sun bayyana cewa da yawan daliban da suka zabi shiga wannan kwas din sun gamsu da abin da suka gani.

To sai dai kuma a wuri daya, lokacin da aka sa na sauraren wanna karar bai zo wa shi Trump da dadi ba , domin yazo a dai-dai lokacin da yake haramar kama ragamar mullkin Amurka.

Dama a wani lokaci can baya sailin da yake tsakiyar yakin naman zabe, Trump ya bayyana shakkun sa cewa zaiyi wahala alkalin yayi masa adalci domin ko yana da nasaba da jinin kasar Mexico

XS
SM
MD
LG