Lauyoyin da ke kare Shugaban Amurka Donald Trump, na shirin kammala gabatar da hujjojinsu a yau Talata, a zaman sauraron batun tsige Shugaban na Amurka da ake yi a Majalisar Dattawan kasar.
Hakan na zuwa ne yayin da batun ko shin za a yadda a saurari bahasin shaidu a yayin wannan zama ke dada karfi ko akasain hakan.
Tawagar lauyoyin da ke kare shugaba Trump, ta kwashe kusan tsawon jiya Litinin tana ta zargin ‘yan Democrat da amfani da tsigewa, a matsayin wani makami na kawar da wani Shugaban kasa da ba sa kauna.
Kenneth Starr, wani dan tawagar lauyoyin da ke kare shugaban kasa din, ya ce tsigewa ta zama tamkar makamin siyasa da jam’iyyu ke amfani da shi kan jun.
Sannan ya ce ‘yan jam’iyyar Democrat a Majajisar Wakilai sun tsige Trump ba tare da goyon bayan dukkan bangarori ba.
Starr shi ne lauyan nan mai zaman kansa, wanda binciken da ya yi ya kai ga tsige Shugaba Bill Clinton a 1998 saboda karyar da ya shara wa masu taya alkali yanke hukunci a tabargazar lalatarsa.
A wani karin rahoto kuma ma’aikatar Shari’ar Amurka ta karyata wani labarin da Jaridar New York Times ta wallafa cewa tsohon mai bayar da shawara kan tsaro John Bolton da Attoni-Janar William Barr sun nuna damuwa game da yanayin Shugaba Trump da kuma alamomin da ke nuna cewa ya na alfarma ma shugabannin China da Turkiyya.
“Sam babu wata tattaunawar da aka yi game da ‘alfarma ga wani’ ko ‘kokarin sa baki,’ a binciken da ake yi, kuma babu inda Attoni-Janar Barr ya ce tattaunawar da Shugaban kasa ke yi da shugabannin kasashen waje bai dace ba,” a cewar mai magana da yawun ma’aikatar ta Shari’a Kerri Kupec a wani sakon Twitter da ya tura yau Talata.
Jaridar ta Times ta kafa hujjar labarinta ne da bayanan da wasu mutane suka yi kan abin da littafin da Bolton ke shirin kaddamarwa ya kunsa.
Za ku iya son wannan ma
-
Yuni 06, 2023
NIJAR: Yawan Matan Da Ke Mutuwa A Yayin Nakuda Ya Ragu.
Facebook Forum