Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lauyoyin Trump Sun Bashi Shawara Kada Ya Yi Hira da Mai Binciken Zaben 2016


Shugaban Amurka Donald Trump .

Jaridar New York Times ta ruwaito cewa lauyoyin shugaba Trump sun bashi shawara kada ya yi hira da Robber Mueller dake binciken zargin katsalandan da aka ce Rasha ta yi a zaben 2016 da kuma yiwuwar cewa shugaban ya karya doka wajen tsige James Comey

Lauyoyion shugaba Donald Trump sun bashi shawara kada ya yarda ya zauna yayi wata hira da mai bincike na musamman Robert Muller, kamar yadda jaridar New York Times ta ruwaito.

‘Yan kwamitin binciken na Muller, sun riga sun tattauna da jami’ai da dama a fadar shugaban kasa ta White House da kuma wasu dake da hannu a yakin neman zaben shugaba Trump, a wani bangare na binciken da ake akan zargin katsalandan da aka ce Rasha ta yi a zaben shugaban kasar Amurka na shekarar 2016, da kuma duba ko watakila Shugaba Trump ya karya doka wajan korar tsohon shugaban hukumar binciken manyan laifukka ta FBI James Comey daga aiki.

Rahoton ya kara da cewa lauyoyin sun bayyana cewa bai kamata mai bincike Muller, ya yiwa shugaban tambayoyi akan wasu sassan binken ba.

A can baya dai, shugaba Trump, ya nuna cewar a shirye yake ya gana da mai binciken na musamman, koda yakle kuma yace shi bai ga dalilin daya sa za a dauki wannan mataki ba, tunda shi bai yarda akwai hadin baki tsakanin kwamitin yakin neman zabensa da kasar Rasha ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG