Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Laylah Othman Ta Yi Sabon Da Bafillace, Har Ta Dauki Nauyin Karatunsa


Laylah Othman tare da Aliyu da 'yan uwansa (Facebook/Laylah Othman)

A duk lokacin da za a yi maganar tabarbarewar tsaro a Najeriya, musanman a arewacin kasar a wannan lokaci, mayuwaci ne a kammala zancen ba tare da an yi maganar al’ummar Fulani ba.

Batun garkuwa da mutane domin neman kudin fansa da kai hare-hare, a wasu lokutan, na ramukon gayya, matsaloli ne da yanzu suka addabi arewacin Najeriya, wadanda kuma ake samun wasu Fulani da hannu a ciki.

Shin ina asalin matsalar? Ko daukar nauyin karatun wani Bafillace da Laylah Aliyu Othman, wata mai aikin jin kai a Najeriya, ya na daga cikin hanyoyin da ya kamata a bi domin kai wa Fulani dauki a wannan mawuyacin lokaci?

Masu sharhi su na gani rashin ilimi ya na daga cikin dalilan da suka sa shigar wasu Fulani cikin harkar garkuwa da mutane da hare-hare ya zama mai muni sosai.

Fulani masu garkuwa da mutane
Fulani masu garkuwa da mutane

Ko da yake, wasu da dama na ganin, rashin ilimi ba hujja ba ce da za ta sa mutum ya dauki makami.

Al’ummar Fulani na daya daga cikin al’ummomi da suka fi ci baya a bangaren ilimin zamani da na addini a arewacin Najeriya musanman a wannan zamani.

Akasarin al’ummar ta na rayuwa ne a wajen birane ko cikin daji inda ba kasafai gwamnati ta ke gina makarantu ba.

Karin bayani akan: Fulani, Bafillace, Laylah Aliyu Othman, Facebook, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Wannan ya sa ko da makiyaya su na son ilimantar da ‘ya’yansu, ba sa iyawa saboda rashin makarantu.

Akwai shirye-shirye da wasu gwamnatoci, ciki har da gwamnatin tarayya a Najeriyar suka bullo da su a baya domin ilimantar da ‘ya’yan makiyaya, yayin da kuma suke ci gaba da zuwa kiwon dabbobinsu.

Shanun Fulani Makiyaya
Shanun Fulani Makiyaya

Sai dai shirye-shiryen da dama ba su haifar da babbar nasara ba, saboda rashin yi da gaske daga bangaren gwamnati.

A shafinta na Facebook, Laylah Aliyu Othman ta wallafa wani hoto wanda ta ce na wani Bafillace ne dan shekara 12 da mahaifina, bayan da ta samu nasarar shawo kan iyayen yaron da su ba ta shi domin ta sanya shi a makaranta.

Laylah ta ce sun ga yaron ne a galabaice a zaune a karkashin wata bishiya a kusa da ofishinta dake Wuse 2 a Abuja, babban birnin Najeriya, azumi ya na dukan shi har ya na shirin ajiye azumin, a wani yanayi da ya nuna yaron yana cikin mawuyacin hali.

“Na gan shi ne a zaune a karkashin bishiya kamar ba ya jin dadi, sai wani ma’akacina ya tambaye shi me ke damunsa, sai ya ce ya karya azuminsa ne saboda ba ya gani.” Laylah ta rubuta a shafinta na Facebook a ranar Alhamis.

Dubban masu bibiyar Laylah a shafinta na Facebook ne suka yi tururuwar sanya ma ta albarka da fatan alheri, tare da yin kira ga sauran jama’a da su yi koyi da ita.

“Sai na sa aka kira shi,” Laylah ta ci gaba da cewa, “ya na shigowa sai na ji ya kwanta min a rai, sai na tambaye shi ko ya na so ya je makaranta, ba tare da bata lokaci ba ya ce yana so.”

A cewar Laylah, ta tambayi matashin mai su na Aliyu, adireshin gidansu da lambar wayar mahaifinsa kuma nan da nan ya ba ta.

“Mun yi ta kai ruwa rana da mahaifansa, har ta kai ga ina ta ziryar zuwa gidansu, don su amince. A karshe dai sun amince.” In ji Laylah.

Laylah da "'ya'yanta" biyu da take daukan nauyin dawainiyarsu
Laylah da "'ya'yanta" biyu da take daukan nauyin dawainiyarsu

“Saboda haka, yanzu gobe zai fara makaranta insha Allah.”

A cewar Laylah, yaranta biyu maza, wadanda su ma dauko su ta yi kamar wannan matashin Bafillace, sun yi farin cikin haduwa da Aliyu mai shekara 12.

“Yanzu ina da kyawawan yara uku.” Laylah ta rubuta a karshe.

A lokacin rubuta wannan rahoto, wannan sako da ta wallafa ya samu tsokaci sama da dubu hudu cikin ‘yan sa’o’i kalilan.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG