Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lee Kuan Yew Na Singapore Ya Rasu


FILE - Former Singapore Prime Minister Lee Kuan Yew (LKY) smiles as he attends the LKY School of Public Policy 7th anniversary dialogue session in Singapore September 14, 2011.

Firai Ministan Singapore Lee Kuan Yew ya rasu yana mai shekaru 91.

Rahotanni daga Singapore na cewa tsohon Firaministan kasar Lee Kuan Yew ya rasu, yana da shekaru 91.

Sanarwar mutuwar ta fito ne daga ofishin Firai Minista na yanzu kuma dan marigayin Lee Hsien Loong, inda ta bayyana cewa Mr. Yew ya mutu ne cikin kwanciyar hankali.

Kafin mutuwar ta sa, an dai kwantar da shi a babban asibitin Singapore a farkon watan Fabrairu saboda fama da ya yi da cutar matsananciyar mura inda aka saka shi akan na’urar nan mai tallafawa numfashi.

Yayin da ya ke jawabi game da rasuwar mahaifin nasa ga ‘yan kasar ta kafar talabijin, Firai Minista Lee Hsien Loong ya zubda hawaye inda ya kwatanta mahainfin nasa a matsayin wanda ya baiwa ‘yan kasar kwarin gwiwa da hada kansu waje guda tare da samar wa da kasar ‘yan cin kanta.

Mr. Lee ya kasance shi ne Firai Ministan kasar na farko a shekarar 1959 bayan da ta samu ‘yancin kai daga Burtaniya inda ya rike ragamar mulki har zuwa shekarar 1990.

Duk da bunkasa da tattalin arzikin kasar ya samu a lokacin mulkinsa, Mr. Lee ya kwashe shekaru da dama yana fuskantar suka daga bangaren ‘yan adawa da suke zargin shi da gudanar da mulkin kama karya.

Sai dai a lokacin Mr. Lee ya ce, kasa ba ta bunkasa dole sai an takaita dokokin da suka ba da damar yin bore da furta fadin ra’ayi a baina jama’a, domin hakan ne kadai zai kawo daidaito.

Yanzu haka hukumomi a kasar ta Singapore sun ayyana zaman makoki daga yau har zuwa ranar lahadi mai zuwa da za a yi jana’izarsa.

XS
SM
MD
LG