Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Libiya ta jinkirta zabe saboda matsalar tsaro


Shugaban Hukumar Zaben Libiya, Nur al Abbar

Libya ta dage zabenta mai tarihi zuwa watan gobe, don ta shirya sosai wa zaben na ta na farko tun bayan hambarar da dadadden shugabanta mai kama karya

Libya ta dage zabenta mai tarihi zuwa watan gobe, don ta shirya sosai wa zaben na ta na farko tun bayan hambarar da dadadden shugabanta mai kama karya, Muammar Ghaddafi, wanda aka kashe daga bisani a mummunan boren bara.

Ofishin MDD da ke Libiya yay aba da jinkirta zaben Majalisar Tarayyar wanda ada za a gudanar ran 19 ga watan Yuni, wanda a yanzu za a gudanar ran 7 ga watan Yuli, da cewa hakan zai samar da isasshen lokaci don kammala muhimman shirye-shirye na zaben.

A wata takardar da ta fitar ranar Lahadi, Jakadan MDD Ian Martin ya ce Hukumar Zaben Libiya ta yi rawar gani ainon musamman idan aka yi la’akari da karancin lokaci da kuma kalubalen tsaro.

Rashin yanayin tsaro masu kyau a wasu sassan Libiya na matukar tayar da hankalin masu shirya zaben. Wani gurnetin da aka harba da roka ya tabi wata tawagar diflomasiyyar Burtaniya a birnin Benghazi ranar Litini, ya raunata wasu dogarawan tsaro biyu, har ilayau kuma wasu mahara sun tayar da bam a makon jiya a wannan birnin, daura da ginin diflomasiyyar Amurka.

Wani kalubalen kuma da masu shirya zaben ke fuskanta shi ne rashin harkar gwamnati mai tasiri a Libiya tun bayan Ghaddafi.

Majalaisar Tarayyar da za a zaba a watan gobe za ta yi aikin rubuta sabon kundin tsarin mulki, da kafa gwamnatin da za ta gaji Majalisar Shugabancin ta Kasa, wadda ba zababba ba ce, wadda ta yi ta jagorantar kasar tun bayan hambarar da Ghaddafi.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG