Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

LIBYA: An Gano Wani Kabari da Gawarwakin Mutane 36 Cikinsa a Benghazi


'Yan kungiyar agajin Red Crescent ta Libya suka tono gawarwakin
'Yan kungiyar agajin Red Crescent ta Libya suka tono gawarwakin

Wata tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta gano kabari dauke da gawarwakin mutane 36 a Benghazi da ake kyautata zaton an kashesu ne a lokaci daya

An gano wani kabari makare da gawarwakin mutane 36 a kusa da birnin Benghazi a kasar Libiya.

Da alamar kashe mutanen aka yi a lokaci guda, to amma ba a san ko su waye mamatan ba. Wani rahoto na cewa wasu daga cikin gawarwakin na saye da tufafin ‘coat’ a yayin da wasu kuma ke sanye da kayan wasan guje-guje.

Ghassan Salame, Shugaban tawagar Majalisar Dinkin Duniya, MDD a Libiya, ya fadi a wata takarda bayani cewa “wannan aika-aikar ta bakanta ma ni rai” ya na mai kiran da a yi binciken al’amura irin wannan.

Duka gwamnatocin Libiya biyu kishiyoyin juna: da wadda duniya ta amince da ita da kuma wadda ke karkashin jagorancin Khalifa Haftar, duk sun yi tir da kashe mutanen, sun kuma yi kiran da a yi bincike.

Libiya ta kasance cikin rudami da dambarwar siyasa tun bayan kashe dadadden shugabanta mai mulkin kama karya Moammar Gadhafi a 2011.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG