Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Libya: Dakarun Khalifa Haftar Sun Karbe Ikon Birnin Sirte


Ministan Libya Mohamed Taha Siala yana ganawa da wakilan jami'an wasu kasashe.

Dakarun da ke biyayya ga babban Hafsan sojin kasar Libya Khalifa Haftar sun ce sun karbe ikon birni mai muhimmanci na Sirte, daga gwamnatin da yammaci ke marawa baya a Tripoli.

Mai magana da yawun sojin kasar ta Libya na Haftar, ya fada a jiya Litinin, cewa sun kwace birnin a cikin ‘yan sa’o’i, kuma tuni da ya sami cikakken ‘yanci.

Kawo yanzu Tripoli ba ta yi wani sharhi akan lamarin ba, haka kuma babu cikakken bayani akan gwabzawar.

Sirte da ke kan gabar Meditareniya, birni ne mai muhimmanci, domin kuwa dakarun na Haftar ne da ikon gabashin sa, yayin da Tripoli take iko da yankin har zuwa yammacin sa.

Birnin yana kuma kusa da yankunan hako mai. Sirte shi ne garin haihuwa na tsohon shugaban mulkin kama karya Moammar Gadhafi, kuma yayi zama a karkashin ikon kungiyar IS, kafin gwamnati ta kwato shi daga hannun masu tsattsauran ra’ayin addini, tare da goyon bayan Amurka.

Libya ta dade tana fuskantar tashe-tashen hakali tun sa’adda aka hambaradda Gadhafi aka kuma kashe shi a shekara ta 2011. Dukkan kokarin daidaita siyasar kasar sun tashi a tutar babu.

Bangarorin 2 suna yaki da juna ne don neman iko da Tripoli tun a watan Afrilu, lamarin da ya rutsa da dubban fararen hula.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG