Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Likitoci 20 Sun Mutu Sakamakon COVID-19 a Abuja a Kwanan Nan


Kungiyar likitocin Najeriya ta kasa da ake kira NMA a takaice reshen babban birnin taraiyya Abuja ta koka a sakamakon rasa mambobinta 20 a makon da ya gabata a dalilin kamuwa da cutar coronavirus.

Shugaban kungiyar likitocin ta NMA Enema Amodu, ya ce sake samun hauhawar masu kamuwa da cutar a matsayin zagaye na biyu da kuma rashin gaskiya daga bangaren marasa lafiya su suka jefa likitoci da ma'aikatan jinya a cikin babbar barazanar kamuwa da cutar.

Dr. Enema ya ce lokuta da yawa marasa lafiya ba sa zuwa gwaji soboda haka ba sa sanin suna dauke da cutar kafin su zo asibiti neman magani idan sun fara rashin lafiya.

To sai dai tsohon shugaban hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta kasa Farfesa Abdulsalam Nasidi ya ce a matsayinsu na kwararru a fanin kiwon lafiya, sun samu wannan labarin kuma suna kokarin yin bincike a kai. Nasidi ya ce ko likita daya aka rasa abu ne mara dadi kuma ya bayyana karfin bazuwar cutar duk da kokarin da mahukunta ke yi wajen shawo kanta.

Amma ga kwararren likita mai zaman kansa a Abuja Dr. Abu Yazid, ya na ganin faruwar hakan na nuna cewa akwai matsala a wani bangaren, ko ta fannin likitocin ko kuma ta wurin gwamnati.

Dr. Yazid ya ce dole ne likitocin su tabbatar cewa suna samun kariya a duk lokacin da za su yi hulda da mara lafiya, sannan kuma hakkin gwamnati ne ta tabbatar cewa likitoci da masu jinyar marasa lafiya suna da kayan aiki da zai rika kare su a lokacin da suke gudanar da aikin duba marasa lafiya. Yazid ya kuma kara da yin kira ga gwamnati da ta tashi tsaye wajen yaki da wannan cutar.

A halin yanzu dai Ministan babban birnin taraiyya Mohammed Musa Bello, ya bada umurnin rufe dukkanin wuraren shakatawa da gidajen nishadi a kokarin dakile yaduwar cutar da ta dawo da karfinta a 'yan kwanakin nan, inda ta kai ga birnin Abuja ya zama na biyu bayan Jihar Lagos a yawan wadanda suka kamu da cutar.

Ga rahoton Medina Dauda cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

XS
SM
MD
LG