Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Likitoci a Zimabwe Sun Tsunduma Cikin Yajin Aiki


Wasu likitoci a Zimbabwe wadanda suka taba yin takin aiki a kwannan baya
Wasu likitoci a Zimbabwe wadanda suka taba yin takin aiki a kwannan baya

A Zimbabwe, likitoci da nas-nas sun shiga yajin aiki, inda suka sha alwashin ba za su koma bakin aiki ba, har sai an ba su kayayyakin kariya saboda su samu damar kulawa da wadanda ke dauke da cutar Coronavirus.

Kwararru a fannin lafiya sun ce muddin ba a dauki matakin shawo kan wannan matsala ba, akwai yiwuwar kasar ta Zimbabwe ta zamanto tungar masu fama da cutar ta COVID-19.

Likitico da nas-nas din sun tsunduma yajin aikin ne, bayan da suka yi ikrarin cewa, hukumomi sun yi biris da bukatun da suka mika na sama musu matakan kariya daga kamuwa da cutar ta Coronavirus.

Batun dai ya taso ne, bayan da wani fitaccen mai gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin da ake kira Zororo Makamba ya rasu a ranar Litinin a wani asibiti da aka ware domin masu fama da cutar.

Iyalansa sun yi korafin cewa babu kayayyakin aiki a asibitin da za su ba da damar kulawa da Makamba, inda likitocin suka ce ba su da rigunan kariya da ababan rufe fuskokinsu.

Fortune Nyamande, wani mai sharhi ne kan al’amuran da suka shafi lafiya

Ya ce, “wannan lokaci ne da ya kamata a ce hukumomi sun daura damara wajen ganin sun kula da jin dadin ma’aikatan lafiyarsu.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG