Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Likitoci Na Barazanar Shiga Yajin Aiki A Najeriya


Tsohon hoto: Likitoci a FMC Yola suna raba tagwayen da aka haifa a manne da juna
Tsohon hoto: Likitoci a FMC Yola suna raba tagwayen da aka haifa a manne da juna

Wasikar ta nuna cewa, kungiyar ta ba gwamnati wa’adin nan da zuwa babban taron da kungiyar za ta yi tsakanin 24 zuwa 28 ga watan Janairu don ta dauki mataki.

Kungiyar likitocin da ke neman kwarewa ta Najeriya NARD, ta yi barazanar shiga yajin aiki a duk fadin kasar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito shugaban kungiyar Dr. Emeka Innocent Orji cikin wata wasika da ya aikewa Ministan lafiya Dr. Osagie Ehanire yana cewa, za su fara shirye-shiryen tsunduma yajin aiki a wannan wata na Janairu idan ba a biya musu bukatunsu ba.

Wasikar ta nuna cewa, kungiyar ta ba gwamnati wa’adin nan da zuwa babban taron da kungiyar za ta yi a tsakanin 24 zuwa 28 ga watan Janairu don ta dauki mataki.

“Mun tsara gudanar da babban taronmu a tsakanin 24 zuwa 28 ga watan Janairu, kuma akwai alamu da ke nuna cewa, idan ba a biya mana bukatunmu ba kafin wannan taro, akwai yiwuwar mambobinmu su ba mu umarnin mu fara shirye-shiryen da zai kai ga shiga yajin aikin gama-gari.” Kungiyar likitocin ta ce, kamar yadda Trust ta ruwaito.

Kungiyar likitocin ta NARD na neman gwamnati ta biya su wasu kudaden alawu-alawu da ba a biya ba, da duba adadin kudaden da aka ware don gudanar da ayyukan horar da likitoci da sauransu.

XS
SM
MD
LG