Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Likitoci Sun Raba 'Yan Biyu Da Aka Haifa Manne Da Juna a Najeriya


Wadansu yara da aka haifa a manne ta ka a Bangladash
Wadansu yara da aka haifa a manne ta ka a Bangladash

A Najeriya wasu ‘yan biyu da aka haifa manne da juna daga kirji da ciki yanzu suna nan suna rayuwasu, ‘yan makonni bayan da aka rabasu a wani asibitin gwamnati.

Kwararru a fannin kiwon lafiya sun ce wannan aikin tiyata na raba yaran aiki ne mai matukar rikitarwa da aka taba yi wajen raba ‘yan biyu a Najeriya.

An yi wani taro a birnin Abuja domin sanar da samun nasarar raba ‘yan biyun mata ‘yan watanni 17 a duniya, Goodness da Mercy, tare da gudanar da wani kwarya kwaryan buki.

Mahaifiyar ‘yan biyun, Mariam Martins, tace ba ta ji dadi ba lokacin da ta fahimci jariranta a hade suke. Ta ce ba a iya gano halin da suke ciki ba lokacin da take da ciki.

Ta ce “dukkan hotunan cikin da aka dauka basu nuna cewa a hade suke ba. Likitocin ma basu san cewa yaran a hade suke ba, sun fada min dai yaran suna wuri guda, suna amfani da mahaifa ‘daya.”

Bayan da aka haifi yaran ta hanyar tiyata, an kai yaran zuwa asibitin gwamnati daga asibitin da aka haife su a jihar Nasarawa.

Inda a asibitin ne likitocin yara da kwararrun likitoci suka yi nazarin yaran har na tsawon shekara kafin su fara shirin raba su.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG