Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Likitoci 'Yan Asalin Najeriya Na Zargin Ana Bautar Da Su A Burtaniya


Wani likita bakar fata
Wani likita bakar fata

Wasu likitoci 'yan asalin Najeriya da suka koma aiki da asibitocin Turai sun koka kan yadda ake mayar da su tamkar bayi a Burtaniya.

WASHINGTON, D.C. - Sakamakon wani bincike da Sashen Binciken Kwakwaf na BBC ya gudanar, ya nuna cewa likito 'yan asalin Najeriya da ke aiki a asibitoci masu zaman kansu a Burtaniya an mai da su tamkar bayi. Hasali ma, akasari wulakancin da su ke sha ya fi wanda su ka gani a Najeriya.

Rahoton, wanda jaridar Aminiya ta buga labari a kai, ya ce daya daga cikin likitocin mai su na Augustine Enekweci, wanda ke aiki a wani asibiti mai zaman kansa mai suna Nuffield Health Leeds, ya ce shi ji ma ya ke kamar a asibitin wani kurkuku ne kawai saboda tsabar azabar da ya ke sha.

Ya ce aiki ya ke yi na kusan tsawon sa'o'i 24 a mako, sannan bai da damar ya dan bar harabar asibitin zuwa wani wurin da ke kusa ya dan mike kafa. Ya ce wani sa'in ma ya na tsaron cewa gajiya na iya sa ya rasa natsuwar duba marasa lafiya yadda ya kamata.

To sai dai, kamar yadda ya kan faru, hukumar asibitin ta yi watsi da wannan zargin, ta na mai dagewa cewa asibitin na kulawa da walwalar likitocin, wadanda su na aiki ne bisa tsarin karba-karba tare da bin dukkan hanyoyin ganin ba a gajiyar da likita ba. Ta ce ta na ba da muhimmanci ga lafiyar ma'aikatanta yadda ya kamata.

Kamar akasarin sauran likitocin da ke korafi, Dr. Enekwechi ya samu aiki ne ta wurin wani kamfani mai suna NES Healthcare, wanda sananne ne wajen daukar likitoci daga kasashen waje zuwa Burtaniya.

Binciken na BBC ya gano cewa kusan kashi 92 cikin 100 na irin wadannan likitocin da aka kawo daga kasashen waje, musamman ma Najeriya, na korafi irin wannan, kuma kashi 81 cikin 100 daga likitocin da ke korafin sun fito ne daga Najeriya.

Misali, wani likita mai suna Femi Johnson ya ce ya na aiki na tsawon sa'o'i 16 a wuni, sannan bisa tsarin ma ana ma iya kiransa na gaggawa a koda yaushe. Dr. Femi ya ce idan ka bukaci hutu yadda ya kamata, sai a ce za a cire kudin sa'o'in da ka huta a biya wanda zai yi aiki a madadinka. Wato korafe korafen sun yi gama da juna.

Wannan ya sa Kungiyar Likitocin Burtaniya ta ce al'amarin ya girgiza ta, don haka ta kuduri aniyar ganin cewa asibitocin sun koma bin tsarin aiki irin na gwamnatin kasar saboda a tabbatar da adalci.

- Jaridar Aminiya

XS
SM
MD
LG